Ace Your Exams: JAMB, Mock, and WASSCE Tips | Scholarships, Biography, Studying and Literature Insights Abin Da Zakayi Idan Layin Wayarka Ya Dade Bayan Rajistar NIN a 2025

Abin Da Zakayi Idan Layin Wayarka Ya Dade Bayan Rajistar NIN a 2025

Yadda Zakayi Idan Kana Ɗaya Daga Cikin Waɗanda Aka Toshe wa Layi.

Abin Da Zakayi Idan Layin Wayarka Ya Dade Bayan Rajistar NIN a 2025

Abubuwan Da Zakayi Idan Aka Dode Maka Layin Wayar Hannunka Bayan Ka Saka NIN Ɗinka.


Ƴan Nigeria sun fara koka wa a dalilin rufe musu layukansu na sadarwa da akayi a cikin kwanakin nan.

 Da yawan mutane sun koka akan wannan al'amari na rufe musu layi da akayi, wasu da yawa sun nemi mafita akan wannan matsalar.

Wannan ya faru ne a ranar 4 ga watan Afrilu hukumar da ke kula da al'amuran sadarwa ta ƙasa wato Nigerian Communication Commission (NCC.) Ta yi wata sanarwar mai ƙarfi, inda ta bada umarnin dukan kamfanonin sadarwan su rufe layukan waɗan da basu yi rajista ba. Nan take kuwa kamfanonin suka ɗauki matakin da aka umurce su da su yi.

Wannan dalilin ne yasa ƴan Nigeria suka fara fuskantar matsalolin kiran ƴan uwansu.

Me Yake Haifar Da Matsalar Rashin Kammala Rajistan Layi.

Mutane da yawa sun koka kan cewa sun yi rajista to amma hakan bai hana an toshe musu layukansu ba. Ga dalilan.

Kamar yadda yake tun lokacin da aka yi wannan sanarwa ta toshe layukan, kusan layuka Miliyan Saba'in da biyar 75M aka toshe na ƴan Nigeria. 

Amma dai matakin ya shafi mutanen da ke cewa sun yi rajista tun kafin toshe layukansu.

Wani babban jami'i yayi bayanin dalilin da ke hana yiyuwar rajista ko da kuwa ka yi.

Ga dalilan;

• Ba mamaki ba a kammala rajistar ba ne.

• Kuskure daga na'urar Kwamfutar na iya haifar da wannan matsalar.

• Yana yiyuwa an haɗa lambar zama ɗan ƙasa da suka cika layuka da yawa.

• Rashin iya haɗa layukan wuri guda daga hukumar NIMC.

• Da kuma, Yankewar Sabis

Ga Abinda Zakuyi Idan Aka Toshe Muku Layukanku.

Babban jami'in ya ce abu na farko da zaka fara yi idan aka toshe maka layinka shi ne ka ziyarci ofishin da ka sayi layin.

Ya ce ba wai son su ba ne su rufe layukan domin hakan ba ƙaramar faɗuwa ba ce a gare su. Kamfaninsu na buƙatar ƙarin abokan hulɗa ba wai raguwarsu ba.

Kafin Ku Fara Yin Rajistar Layinku Da Haɗa Shi Da Katin Ɗan Ƙasa Ga Abinda Ake Da Buƙata.

• Lambarka ta wayar salula.

• Imel Adireshinka.

• Cikakken Sunanka da na mahaifinka.

• Kwanan watan da aka haifeka.

•. Lambarka ta zama ɗan ƙasa idan ka rasa ta kuma zaka iya danna *346# domin gano ta.

Yadda Ake Hada Lambar Waya Da Lambar Dan Ƙasa Na Kowane Layi.

Na MTN;

Da farko ka ziyarci shafinsu na yanar gizo mtnonline.com/nin/ sai ka cike wani fom da zasu baka. 

Ko kuma ka danna *785# ka saka lambar ɗan ƙasa.

Na GLO;

Abin da zakayi zaka fara tura saƙon waɗan can abubuwan da na lissafo zuwa ga 109. 

Na AIRTEL;

Zaka danna *121*1# sai ka rubuta Lambobi sha ɗaya 11 na ɗan ƙasa ka tura.

Na 9MOBILE;

Da fari ka ziyarci shafinsu na yanar gizo 9mobile.com.ng /nin

Zasu gwada maka wani fom sai ka cike. Sai ka latsa wani koren wuri inda aka rubuta Verify and Link Your NIN now.

A halin yanzu ma'aikatar sadarwa ta hana karɓan kuɗi ₦20 idan akayi binciken lamabar zama ɗan ƙasa. Don haka kowa zai iya bincikawa kyauta.

Post a Comment

0 Comments