Ace Your Exams: JAMB, Mock, and WASSCE Tips | Scholarships, Biography, Studying and Literature Insights Cikakken Bayani Game Da Aljanin Bacci Ɗan'dannau A Addini Musulunci Da Kuma A Kimiyance

Cikakken Bayani Game Da Aljanin Bacci Ɗan'dannau A Addini Musulunci Da Kuma A Kimiyance

 Cikakken Bayani Game Da Aljanin Bacci Ɗan'dannau A Addini Musulunci Da Kuma A Kimiyance

Cikakken Bayani Game Da Aljanin Bacci Ɗan'dannau. 


Ka taɓa fuskantar ƙalubale a wurin baccinka wanda har ta kai ga baka iya motsi ka kadan? Lokuta da dama wasu mutanen sukan yi bacci a cikin baccin nasu sai suji an dafe musu kirji ko kuma maƙoshi har su kasa farkawa daga baccin da suke yi.

Masana da dama sun yi cikakken bayani akan wannan dannewar da ake yi a lokacin da ake yin Bacci. Mafi yawanci hakan yafi faruwa ne a lokacin da mutun zai farko daga dogon bacci da yake yi.

Idan masu karatu na biye da mu zai fahimci mene ne asalin Dannau.

Wani babban Likita dake koyarwa a garin Yobe a arewa maso gabas wato Dakta Babagoni Woru yayi cikakken bayani akan Dannau a lokacin da BBC Hausa suka zanta da shi. 

Babban Likita Babagoni Woru ya ce Dannau na faruwa ne a lokacin da mutun yazo farkawa daga baccin da yake yi. A daidai wannan lokacin mutun yakan ji jikinsa babu karfi haka kuma zai ji ya kasa motsawa ko kaɗan kuma zai ji kamar ana danne masa gaba ana hana shi numfasawa.

Likitan yace, wasu lokutan ma sai kaji kana son kayi ihu domin ka kwaci kanka amma sai kaji ba zaka iya ba. To amma mafi yawancin kasashenmu dake tasowa waɗanda suka fi yarda da al'ada da kuma addini haka kuma basu da masaniya akansa kamar yadda ilmin kimiyya ya bayyana.

Mallaman Addini sun bayyana dannau a matsayin wani sihiri wanda yake tasiri a wurin wanda baya addu'a a lokacin da zai yi bacci. 

Mallam Hayatu Umarari wanda ke zaune a birnin Maiduguri a garin Borno yayi wa BBC Hausa bayani game da Dannau cewa bakomai ba ne face bakaken aljannu masu hana wa waɗanda basa addu'a a yayin da zasu yi bacci.

Mafi yawanci sun fi takurawa mutanen da basa addu'a a lokacin bacci sai su hau kirjinsu ko makogoro su danne su har sai kaji bazaka iya numfashi ba.

Mallamin ya ce abu ne mai kyau domin neman kariyar ubangiji kafin kwantawa bacci kayi addu'o'i kuma ka tabbatar ka yi alwala. 

Post a Comment

0 Comments