Yadda Zakayi Ka Boye Contacts Dinka Duka A Cikin Facebook.
Kamfanin Facebook sun tanadi wani wuri a cikin application ɗinsu domin tanadin Contacts wato numbobin yan uwa da abokanka.
Wannan damar da kamfanin Facebook ya bayar ta dade tana aiki amma ba kowa ne ya san da ita ba, to a yau dai yakamata kusan wannan domin zai amfaneku a wata rana.
Abin da kawai ake bukata shi ne ka tanadi facebook Username wato ka kasance mai amfani da facebook.
Idan ka bude manhajar facebook dinka to sai ka shiga cikin settings.
Daga can kasa gaba ɗaya zaka ga inda rubuta upload contact anan sai ka shiga. Daga nan a can sama zaka ga wani wuri an rubuta upload contact sai ka kunna shi, idan ka kunna shi zai nuna maka wani box an rubuta upload contact wani kuma zai ce import contacts sai ka shiga anan zaka ga contact ɗin naka sun shigo a ciki.
Daga nan sai kayi refresh zai nuna maka Contacts din idan sun shigo. Zaka ga inda aka rubuta view contact you've upload in messenger sai ka shiga ka lura da kyau daga can kasa kadan zaka ga inda aka rubuta view contact in Facebook anan ma sai ka shiga zaka ga contact ɗin naka duka sun shigo.
Duk lokacin da ka rasa waya ko kuma layinka ya ɓata zaka iya dawo da duk wata numba da kake bukata domin ba zasu taba gogewa ba har sai idan kai ne da kanka ka goge su.
Allah yasa kun fahimta.
0 Comments