Ace Your Exams: JAMB, Mock, and WASSCE Tips | Scholarships, Biography, Studying and Literature Insights Aure a Kannywood: Hafsat Idris, Aisha Tsamiya, Hassana Muhammad & Fati Washa

Aure a Kannywood: Hafsat Idris, Aisha Tsamiya, Hassana Muhammad & Fati Washa

 Aure a Kannywood: Hafsat Idris, Aisha Tsamiya, Hassana Muhammad & Fati Washa

Bayan Auren Wasu Jaruman Kannywood, Maganganu Sun Biyo Baya

Bayan auren wasu shahararrun jarumai a masana’antar Kannywood, an samu cece-kuce da maganganu daban-daban daga jama’a. Wasu daga cikin maganganun ba su yi daɗi ba, yayin da wasu kuma suka yi ko oho.

Auren Hafsat Idris

Lokacin da jaruma Hafsat Idris ta yi aure, mutane da yawa sun yi zargin cewa ta auri ɗaya daga cikin ’ya’yan tsohon shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha, kasancewar an dade ana danganta su da soyayya tun da dadewa. Amma daga bisani jarumar ta fito ta yi karin bayani, inda ta ce:

“Ba ɗan Sani Abacha na aura ba kamar yadda mutane suka ɗauka. Aure kaddara ce ta Allah, Shi ne kaɗai yake sanin wanda kowane bawa zai aura. Ba ɗan Sani Abacha kaɗai ne ya nemi aurena ba, don haka kada ku ce na yaudare shi. A’a, haka Allah Ya nufa, ba shi ne mijin da aka kaddara zan aura ba.”

Auren A’isha Aliyu Tsamiya

Haka ma lokacin da jaruma A’isha Aliyu Tsamiya ta yi aure, lamarin ya zo wa mutane da mamaki saboda ba a yi sanarwa ba. Kawai sai mutane suka ga an ɗaura aurenta da ɗaya daga cikin masoyanta. Wannan ya jawo maganganu da dama — wasu suna cewa ba ta gayyaci mutane saboda ba ta son hayaniya, wasu kuma suna cewa rowa ce kawai yasa ta bar kowa a baya.

Ita kuwa ta bayyana da cewa:
“An yi aurena ne a sirrance ba tare da sanin jama’a ba, saboda bana son na takura wa kowa. Kudin mota yanzu sun yi tsada saboda matsalar man fetur da Najeriya take ciki, don haka na ga ya fi dacewa a yi auren cikin sauki ba tare da wahalar da kowa ba.”

Auren Hassana Muhammad da Furodusa Bashir Mai Shadda

Lokacin da jaruma Hassana Muhammad ta auri jarumi kuma furodusa Bashir Mai Shadda, itama ta fuskanci suka da kiran jama’a da dama. Mutane da yawa sun zargi Bashir Mai Shadda da rashin adalci, kasancewar ana ganin yana shirin auren jaruma A’isha wadda aka gansu tare a wani shahararren shiri.

Amma jaruma Hassana ta fito ta fayyace gaskiya, inda ta ce:
“Ba kamar yadda mutane suke tunani ba ne. Babu wata alaƙa tsakaninsu da A’isha bayan harkar masana’antar Kannywood. Hotuna da bidiyoyin da aka gani tsakaninsu da A’isha duk wani shiri ne na talla inda aka zaɓe su a matsayin miji da mata. Amma banda haka babu wani abu tsakaninsu. Bashir Mai Shadda mutum ne nagari, shi yasa nake sonsa. Abinda nake nema a wurinku shi ne addu’a Allah Ya saka albarka a aurena.”

Magana Kan Fati Washa

Shima lokacin da jaruma Fati Washa ta yi wani posting a shafinta na Instagram, mutane da dama sun fara hasashen cewa tana shirin yin aure, kasancewar posting ɗinta ya nuna alamar hakan.

Post a Comment

0 Comments